Yanzu haka dai al’ummomin da lamarin ya shafa na kira ga hukumomin tsaro da a taimaka musu domin kwaso dukiyoyinsu da dabbobinsu dake daji.
‘Yan gudun hijira a Jalingo fadar jihar Taraba sun koka game da halin da suke ciki a yanzu, da kuma neman taimakon hukumomi.
Yanzu haka dai ana ci gaba da samun kwararar ‘yan gudun hijira daga Jalingo har zuwa Mayo-Belwa dake jihar Adamawa.
Alhaji Muhammadu Gongola, dake zama shugaban kungiyar Tabital Puulaku a Taraba, ya ce bukatarsu itace abarsu su debo dukiyoyinsu da aka maida ganima.
Wasu dai na danganta lamarin ne da rikicin Makiyaya da Manoma, batun da ko shugaban kungiyar Miyetti Allah a Taraba Jauro Sahabi Mahmud ke musantawa.
Yayin da ‘yan gudun hijiran ke kokawa da rashin samun tallafi daga gwamnatin jihar Taraba, hukumar kai dauki ta SEMA a jihar ta bakin babban sakataren hukumar Mista Nuvalga Danagbo, ya bayyana matakan da aka dauka.
Ana ta bangaren rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta ASP David Misal, ta sha alwashin zakulo wadanda ke da hannu a wadannan hare-haren.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum