A makon jiya ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan wannan doka a wani matakin na karfafa anniyar gwamnatinsa ta fafutukar kawar da ayyukan rashawa a Najeriya.
To sai dai jiya laraba, ‘yan majalisar wakilan sun zartar da wani kudiri da ke zargin shugaban da yunkurin shiga hurumin ayyukan da kundin tsarin mulki ya shatawa Majalisar dokoki, a don haka tilas ne a dakatar da aiwatar da dokar.
Haka zalika, Majalisar Dattawa ta yi mahawara akan wannan batu, inda ta bayyana lamarin a matsayin wani kutse da bangaren zartarwa ke kokarin yiwa sashin majalisa.
A dangane da haka ne, Majalisar Dattawan ta umarci Atoni Janar kuma Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, ya bayyana a gabanta.
“Wato akwai dan burbushin wani fargar jaji ko siyasa-siyasa,” inji Dakta Nasiru Adamu Aliyu, malami a tsangayar nazarin aikin lauya a Jami’ar Bayero Kano.
“Watakila ko wani misalin kurari ne suke so su yi. Amma ni a ganina, dama can akwai dokokin nan,bibiya ne kurum ba sa yi. Kuma idan ba a bibiya, doka ba za ta yi wani aiki ba. Haka ma ita ma wannan dokar din ba za ta yi aiki ba sai dai a yi amfani da ita don cimma wasu buri.”
Sanata Masa’ud El-Jibril Doguwa wanda ya wakilci shiyyar Kano ta kudu a Majalisar dattawan Najeriya a shekarar 1999 zuwa 2003, cewa yake,
"Majalisa da ita bangaren zartaswa kamata ya yi kowa ya san ina ne huruminsa. Hurumin nan a cikin doka, gashi nan karara, kowa an rubuta, baki da fari cewa, ga irin aikin wane. Saboda haka ba mu san dalilin da yasa a takaice za a dinga samun shishshigi ba.
Ya kara da cewa,
“Majalisa ce take izini ko kuma aka bata hurumin yin doka, su kuma an basu hurumin aiwatar da dokar da aka yi. Idan kuma rigima ta kaceme tsakanin bangarorin biyu, to kamata yayi bangaren shari'a ta shigo domin ta daidaita.”
Yanzu haka dai majalisar dattawan ta kudiri anniyar gudanar da garambawul ga dukkanin dokoki ko kuma wata oda mai nasaba da irin wannan da nufin tabbatar da cewa, ba sa cin karo da sassan kundin tsarin mulki ko kuma wasu dokoki da majalisar kasa ta yi.
Facebook Forum