A yayinda ake sa ran za’a fara jigilar alhazan Nigeria a ranar 21 ga wannan watan, hukumar jin dadin alhazan na ci gaba da daukan matakan dakile duk wata cuwa-cuwa daga ma’aikatan alhazai a matakai danam daban.
Can baya an sha samun matsaloli da suka jibanci cutar alhazai a wasu jihohin kasar.
Alhaji Umar Bala, babban jami’i a hukumar alhazan da ya kai ziyara jihar Niger, domin gudanar da wani taron bita ga ma’aikatan hukumar ya bayyana matsayinsu. Yace ma'aikatan su sani cewa duk aikin hajji amana ne. Duk alhajin da ya biya kudi domin ya yi aikin hajji wajibi ne a kansu, kuma hakkinsa ne su tabbatar ya yi aikin hajjin. Duk ma’aikacin da bai yi aikin da ya kamata ya yi ba, yasani akwai nauyi akansa.
Gwamnatin jihar Niger ma ta ce a bana ta dauki matakin toshe duk wata kafa ta aikata ba dai-dai ba a hukumar jin dadin alhazan jihar domin kaucewa irin abun da ya faru bara.
Alhaji Tanko Baba Ahmed, mai baiwa gwamnan jihar shawara akan harkokin addinai, Ya ce abubuwan da suka faru can baya an zauna an gano dalilan da suka haddasa su.
Sakataren jin dadin alhazan jihar Niger Alhaji Shehu Barwa Beji, ya yi karin haske akan matakin da suka dauka.Duk wanda yake son zuwa hajji sai ya biya kudi a banki a bashi takardar shaida. Sun kuma hana karban kudi tsaba.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Facebook Forum