Yajin aikin ya biyo bayan zanga-zangar lumana da kungiyoyin makiyaya da mahauta da manoma ‘yan kasuwa suka gudanar a farkon makon nan, inda suka nuna fushinsu da yunkurin kafa dokar hana kiwo da ake son kafawa.
Yajin aikin gama-garin da mahauta da dillalan Shanu da na kananan dabbobi suka shiga yau kwana uku ya jefa jama’a da dama cikin wani yanayi, inda ala tilas aka koma neman kifi domin sawa a girki.
To sai dai a martaninsa, gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Isiyaku, wanda ya nuna bacin ransa game da wannan yajin, ya bukaci al’ummar jihar dasu kwantar da hankulansu, inda yace za’a gano bakin zaren lamarin.
Gwamnan wanda ke magana ta bakin hadiminsa kan harkokin yada labarai Mr Sylvanus Giwa, ya ce za’a hau teburin sulhu, to amma ya bukaci kungiyar Fulani Makiyaya da sauran kungiyoyin dake da korafi dasu mika kukansu ga kwamitin da majalisar dokokin jihar ta kafa don zaman jin ra’ayin jama’a, to amma ba bore ba, ko kuma yajin aiki.
Batu na kafa dokar hana kiwo a jihar ya janyo cece-kuce, inda ma ake zargin yan majalisar dokokin jihar da karbar toshiyar baki na miliyoyin Naira, batun da ko shugaban kwamitin harkokin yada labarai na majalisar Hon. Sale Sa’ad ke musantawa.
Ya zuwa yanzu tuni aka sauya akalar tirelolin dake dakon shanu da dabbobi zuwa hanyar Gombe maimakon bi ta Taraba, lamarin da ka iya jawo wa jihar asarar kudaden shiga na miliyoyin naira. Mafindi Umaru Danburam, shine shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihohin Arewa maso gabas ya ce tura ce ta kai ga bango shi yasa suka dauki wannan mataki.
Sarakuna da kuma shugabanin al’umma a jihar na yunkurin shiga tsakani, domin rage radadin da yajin aikin zai ci gaba da janyowa a jihar.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum