Masu zanga-zangar da suka hada da kungiyoyin masu motocin sufuri da kanikawa da masu aikin Walda da kuma masu facin Taya, sun taru gaban Majalisar Dokokin jihar Neja ne domin mika kukansu kan takurawar da suka ce ana yi musu. Amma sai jami’an tsaro suka fatattakesu da barkonon tsohuwa.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Mallam Idris Mohammad, ya ce sun dauki matakinne kasancewar gwamnati ta takura musu, kasancewar duk mambobin kungiyar kowa ya biya kudaden haraji sama Naira dubu talatin, sai gashi gwamnati ta sake turo wani kamfani domin ya karbi haraji.
Kakakin ‘yan sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, ya ce dalilin tarwatsa masu zanga-zangar shine domin sun kashe hanya kimanin awanni biyu babu mai iya wucewa.
Shi kuma kakakin gwamnatin Neja, Mr. Jonathan Batsa, ya ce rashin biyan kudaden haraji shine dalilin kawo ‘dan kwangila domin karbar harajin. Inda yayi kira ga gamayyar kungiyoyin da su zo su zauna da gwamnati domin a tantance.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum