Shugaban hukumar Kwastan mai kula da shiya ta daya, Kwanturola Mohammed Uba Garba ne ya sanar da haka a wani taron manema labrai da ya kira a birnin Lagos.
Kwanturolan ya bayyana cewa akasarin kayayyakin da hukumar ta kama, kayayyaki ne da suka hada da shinkafa da tayoyin mota da ake kira “tokumbo”, da kuma wadansu kayayyaki da aka hana shigowa da su, ko kuma kayayyakin da aka bada izinin shigowa dasu, amma aka yi amfani dasu wajen boye kayayyakin da aka hana shigowa da su.
Ya bayyana cewa, sun kama shinkafa buhu dubu shida da dari uku da hamsin da shida, wanda darajar kudinsa shine Naira miliyan saba’in da takwas, da dari uku da casa’in da biyar. Ya kuma ce, hukumar ta kama ganyen wiwi kunshi dari uku da tamanin da hudu wanda yace an kimanta cewa kudinshi zai iya kaiwa Naira miliyan goma sha takwas dubu dari hudu da talatin da biyu.
Yace akwai kuma tayoyi da aka hana shigowa dasu dubu hudu da dari tara da tamanin da hudu, wanda su kansu adadin kudinsu ya kai miliyan arba’in da biyu. Akwai kuma motoci guda goma sha biyu wadanda kudinsu ya kai miliyan hamsin da takwas da dari takwas da sha tara.
Kwanturola Mohammed Uba Garba ya bayyana cewa, adadin farashin kayan da suka kama ya kai Naira miliyan dari shida da bakwai da dubu dari bakwai da goma sha bakwai da naira dari biyar da talatin da biyar.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Babangida Jibrin ya aiko daga birnin Ikko.
Facebook Forum