Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sule Lamido Akan Rikicin Shugabanci da Ya Addabi PDP


A shepherd guides a flock of sheep through central Madrid, Spain.
A shepherd guides a flock of sheep through central Madrid, Spain.

Kokarin shawo kan rikicin shugabancin jam'iyyar PDP da kwamitin amintattunta ya nema ya yi ya cutura domin duka bangarorin da abu ya shafa kamar babu wanda yake son ya bada kai bori ya hau.

Alhaji Sule Lamido ya fara da cewa idan ana maganar sulhu to ana maganar gyara, dole ne a fita a yi wasu gyare gyare.

Yace bayan an shiga hayaniya daga bangarorin yace shi ya fada bashi da wani bangare. Yace duk bangarorin babu wanda yace ya bar PDP. Yace yanzu babu wanda zai ji kowane cikin masu hayaniyar shugabancin jam'iyyar.

Sun yadda zasu bi dattawa kuma yace sun je wurinsa suna neman a dauki matakan sulhu.Yace suna kan maganar, Bankole Dimeji da Tony Anenih suka shigo. Dukansu sun zauna sun tattauna.

Sun sake zama da gwamnan Bayelsa da mataimakin shugaban majalisar dattawa Ikweremadu da wasu domin su cimma matsaya. Sun yadda a samo daidaito tsakanin Modu Sheriff da Ahmadu Makarfi domin jam'iyyar ta mike.

Sule Lamido yace duk abun da za'a yi a tabbatar cewa ba'a kunyata Modu Sheriff ba ko kuma walakantashi bayan a n kawoshi jam'iyyar kana kuma a ce an koreshi. Kamata yayi a sameshi a tattauna dashi domin a samu masalaha.

Yace duk abun da za'a yi a samu zaman lafiya shi Sule Lamido yana goyon bayansa. Yace yayi imani Sheriff da Makarfi suna kaunar jam'iyyar saboda haka bashi da shakka za'a samu masalaha.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG