Shi dai bangaren Sanata Nasiru Mantu ya amince zai yi aiki da kwamitin gudanar da zabe da aka kafa a karkashin Sanata Ahmed Makarfi.
Amma bangaren Sanata Ali Modu Sherrif ya jajirce akan shi ne da shugabancin jam’iyar.
A makon da ya gabata ne wasu manyan kotunan kasar suka yanke shari’a masu karo da juna kan rikicin shugabancin jam’iyar.
Yayin da wata kotun tarayya ta amince da shugabancin Sanata Ahmed Makarfi a Fatakwal, wata kotu ta daban a Legas mai daraja daya da ta Fatakwal din ta yanke hukuncin Ali Modu Sharrif ne shugaban jam’iyar.
Tun bayan da mulki ya kufcewa jam’iyar a zaben da aka yi a bara, jam’iyar ta PDP ta ke ta fuskantar matsalolin cikin gida.
Domin jin irin cecekucen da aka yi tsakanin bangarorin da ke takaddama da juna, saurari wannan rahoto na Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: