Shugaban jam’iyar Sanata Ali Modu Sherrif ne ya bayyanawa manema labarai a birnin na Fatakwa cewa an dage taron saboda kotu ta ba da umurnin a dakatar da shi.
Jam’iyar ta PDP dai ta shiga wani abu da wasu ke kwatantawa da rudani tun bayan da ta fadi a zaben 2015, lamarin da ya sa shugabanta ya yi murabus daga baya kuma Sherrif ya karbi shugabancin.
Sai dai darewa shugabancin jam’iyar bai yiwa wasu dadi ba, abin da ya sa suka garzaya kotu suna kalubantar shugabanta da ya sauka domin wa’adin da aka dibawa yankin arewa maso gabashin Najeriya ya wuce.
Dama dai gabanin soke taron, bangaren su Farfesa Jerry Ghana da Raymond Dokpesi da ke adawa da Sherrif, ya yi likimo a can birnin Abuja domin ganin yadda taron zai kaya.
Wakilin Muryar Amurka a Fatakwal Lamido Abubakar Sokoto ya tattaro mana ra’ayin wasu ‘yan jam’iyar da suka yi niyyar halartar taron, kan rikicin jam’iyar da kuma batun dage taron: