Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Ta Amince Zata Amshi Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya 4000


Yayin da kasar Sudan ta Kudu ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, jiya Lahadi ta amince ta karbi sojojin kiyaye zaman lafiya 4,000 da Kwamitin Tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince a turo cikin watan da ya gabata.

Shugaba Salva Kiir ne ya amince, wanda cikin watan Agusta yayi tirjiya ga karbar karin sojojin kiyaye zaman lafiya, biyo bayan ziyarar da mambobi 15 na Kwamitin Sulhu Na majalisar dinkin duniya suka kai Juba, babban birnin kasar domin shawo kan manyan jami’an kasar da amincewa.

Sai dai ba a bayyana cikakken jadawalin jarjejeniyar ba, kuma ba a fadi lokacin da za a aika da sojojin ba. Sabbin sojojin da za a aika za su mayar da hankali ne wajen kare fararen hula a birnin Juba, yanzu haka dai akwai sojojin kiyaye zaman lafiya sama da 12,000 a yankin.

A ziyarar da wakilan hukumar tsaro ta majalisar dinkin duniya ke yi Sudan ta Kudu ranar Asabar, sun isa sansanin ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya a babban birnin kasar, inda dubban fararen hula ke zaune cikin tsoron fadan da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin magoya bayan shugaba Kiir da ‘yan tawayen da ke kokarin hambarar da gwamnatinsa.

XS
SM
MD
LG