Jiya Alhamis jami’an ‘yan sanda sunyi sintiri kan tituna a birnin Libreville, bayan arangama da masu zanga zangar da suka cinnawa ginin Majalisa wuta, haka kuma jami’an tsaro suka farma hedikwatar jam’iyyar adawa.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta yi kira ga duk bangarorin biyu su hada kai domin gujewa tashin hankalin da ka iya faruwa nan gaba, a yayin da kuma bata kauda yiwuwar daukar matakin da ya dace ga duk wanda ya aikata laifi ba.
Yayin da ofishin jakadancin Amurka dake Libreville ya fitar da sakon gargadi, domin sanar da duk Amurkawan da ke Gabon tashe tashen hankulan da ke faruwa, ana kuma sanar da su nemi gurare marasa hadari su fake.
Jami’an gwamnati dai sunce a kalla mutum daya ne ya rasa ransa wasu kuma 19 suka sami raunuka. Shugaban jam’iyyar adawa Jean Ping ya fadi cewa akalla mutane biyu suka mutu.