Rahotanin dake fitowa daga kasar sunce masu zanga-zanga sun cinnawa Majalisar Dokokin kasar wuta, inda suka fito dauke da kwalayen da aka yi rubuce-rubucen dake cewa “Dole Ali ya san inda dare yayi mishi.”
Wata jarida ta “Guardian” ta ruwaito cewa ‘yansanda sun harbe mutane ukku, kuma sun kashe su, amma har yanzu gwamnatin Gabon din bata tabattarda maganar ba.
Haka kuma madugun ‘yan adawar kuma dan takaransu na shugaban kasa Jean Ping yace ma’aikatan tsaro sun kadarwa hedkwatar jam’iyyarsa har suka hallaka mutane 2, suka raunana wasu 19.
Yanzu haka dai an baza ‘yansanda ko ina a cikin Libreville, babban birnin kasar.
Haka kuma wakilin Muryar Amurka dake garin, Idrissa Fall, ya ruwaito cewa wasu kwamishinonin Hukumar Zabe ta Gabon din sunyi murabus don nuna rashin amincewarsu da sakamakon da aka bada.