Sai dai tun ba’a je ko’ina ba wadannan jami’o’i sun fara fuskantar cikas saboda dalilai na rashin kudaden gudanarwa kamar yadda a jiya 1 ga watan satumba daukacin jami’oi mallakar gwamnatin kasar suka kammala babban hutu.
Daliban sun shiga yajin daukar darasi na tsawon kwanaki 3 domin tilastawa hukumomi biya masu wasu mahimman bukatu yayinda su ma malaman jami’oi suka yi barazanar dakatar da aiyukan koyarwa muddin ba a biya bashin albashin wasu takwarorinsu ba kafin ranar 8 ga watan satumban nan.
Wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa wannan yajin daukar darasi sun hada da rashin basu alawus alawus kamar yadda maga takardar kungiyar daliban jami’a wato Sallau Shi’abou ya bayyana.
Domin Karin bayani saurari rahoton Sule Mumuni Barma.