Lauyoyin Trump sun shigar da karar wannan ma’aikatar labaran ta Mail Media wacce ta kafa jaridar Daily Mail a Maryland a jiya Alhmais, suna bukatar diyyar dollar miliyan 150 saboda bacin suna wanda lauyoyin suka kwantanta da labari mafi muni da jaridar ta dora a kan shafinta na yanar gizo.
Lauyoyin suka ce a cikin karairayin da jaridar ta watsa, ta ce uwargidan Trump ta yi aikin karuwanci a cikin shekarun 1990 kafin ta hadu da mijin nata.
Suka ce abubuwa da jaridar ta watsa ya yi muni, kuma zai cutar da uwargidan ta Trump don haka tana bukatar diyar dollar miliyon 150, a cewar lauyoyin Trump.
An kai wannan karar ce bayan da jaridar Dail Mail ta fito ta yi bayani ta janye labarin.
A kokarin da jaridar Daily Mail ta yi ta janye wannan labarin, ta ce ba manufarta ce ta ce Uwargidan Trump ta yi aikin karuwancin ba, sai dai abin da ta yi shi ne ta bugo wannan labari ne da zummar bayyana wannan zargin zai iya yin mummunan tasiri akan zaben shugaban kasar koda ma zargin karya ne.