Ma'aikatar tsaron kasar ta ce farmakin ya hada da jiragen saman yaki daga jirgin ruwan Rasha mai dakon jiragen yaki tilo- Admiral Kuznetsov, wanda ya isa gabashin bahar rum a makon da ya gabata tare da wasu jiragen ruwan.
Farmakin na yau Talata an auna ne kan mayakan sakan ISIS da ake kira Nusra Front, kamar yadda kafofin yada labaran Rasha suka fada.
Wannan yana zuwa ne kuma a dai dai lokcinda 'yan gwagwarmaya suka ce ana ci gaba da kai farmaki da jiragen yaki kan yankin Aleppo dake hanun 'yan tawaye.
A wani lamari da bam kuma, wata kotun Masar ta yi watsi da hukuncin kisan da aka yankewa tsohon shugaba Mohammed Morsi ta kuma bada umurnin a sake duba hukuncin da aka yanke masa mai nasaba da fasa wani gidan yari a lokacin wata arangama da aka yi wadda ta tilastawa tsohon shugaba Hosni Mubarak yin murabus.
Kotun mai watsi da karar ta fada yau Talata cewa wasu mutane biyar da aka yankewa hukunci su ma za a sake masu hsari’a.