Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nan Amurka Ana Cigaba da Zanga-zangar Kyamar Zaben Donald Trump


Masu zanga zangar kyamar zaben Donald Trump jiya a birnin Los Angeles na jihar California
Masu zanga zangar kyamar zaben Donald Trump jiya a birnin Los Angeles na jihar California

Tun makon jiya da mutane masu adawa da zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka suka fantsama titunan birane suna zanga zangar har yanzu basu daina ba.

A halin yanzu kuma,,,ana ci gaba da gudanarda tarukkan zanga-zanga a birane da dama na Amurka don nuna adawa da zaben da aka yi wa Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasar.

Wasu daga cikin biranen da aka gudanarda zanga-zagar a jiya Litinin sun hada da Los Angeles da wasu unguwannin dake kusa da nan Washington, DC inda daruruwan dalibbai suka fito suna maci akan manyan tituna.

Sai dai tarukkan gangamin zanga-zangar na jiya basu kai girman wadanda aka yi jim kadan bayanda Donald Trump ya kada Hillary Clinton a zaben da aka yi cikin makon jiya.

Tun cikin makon jiyan dai Shugaba Obama da Trump suke ta kira akan Amurkawa da su hada kai da juna kuma su baiwa Trump damar ya gwada iyawarsa a shugabancin kasar da zaran ya dare kan karaga a ran 20 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG