A jiya ne wani kakakin MDD, Farhan Haq, yake cewa daga ranar Jumu’a da ta gabata zuwa yau kadai, yawan mutanen da suka rasa muhallansu sun karu da mutane 6,000, kuma galibinsu suna kokarin gudu ne zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da aka baiwa mafaka.
Sojan na Iraq sunce sukan binciken dukkan mutanen dake gudowa daga Mosul don tabattarda cewa basa da wata alaka da kungiyar ta IS kafin a barsu su shiga sansanonin ‘yan gudun hijiran.
Sojan Iraq din, wadanda na jiragen kawancen kasashe da Amurka ke wa jagoranci ke baiwa rufa baya, na kokarin gujewa asaran rayukkan mutane fararen hula da su kansu, yayinda mayakan IS ke ci gaba da anfani da ‘yan kunar bakin wake wajen tada bama-bammai.