Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kawance Sun Kai Hari Kan Dakarun Dake Goyon Bayan Gwamnatin Syria


Jirgin saman yakin kungiyar kawance da Amurka ke jagoranta ya kaiwa dakarun dake goyon bayan Syria hari, dake ci gaba da keta yarjejeniyar daina tashin hankali a wani yankin da aka kebe kusa da wani sansanin sojin da ake horas da mayakan Syria.

Kakakin rundunar soji ta tsakiya Major Josh Jacques ya shaidawa VOA cewa, dakarun dake goyon bayan gwamnatin Syria sun kafa wani ayari a arewa maso yammacin sansanin dake al-Tanf, da motocin yakin Syria, da motoci masu sulke, da makaman atilare, da manyan moticin aiki, suka fara jera motocinsu suna shirin yaki.

Jacques yace, Rundunar hadin guiwar tayi ta shawagi na tsawon sa’oi a sararin sama, har suka harba roka a kasa na gargadi, amma suka ci gaba da jan daga.

Dakarun hadin guiwar sun kuma yi amfani da hanyar sadarwar da aka kafa tsakanin Amurka da Rasha suga ko Rasha zata sa su janye daga wurin, amma kokarin da Rasha tayi sau da dama, bai canza komi ba.

Bisa ga cewar Jacques, Amurka ta kaiwa motocin yakin da kuma buldoza biyu hari. Duk da haka, wadansu dakarun Syria sun ci gaba da zama a yankin da aka haramta ci gaba da tashin hankalin. Ya shaidawa VOA cewa, Muna kira garesu su janye daga yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG