Wani jami’in ofishin ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace jakaden Sedar Kilic ya gana da mataimakin sakataren ma’aikatar Thomas Shannon jiya Laraba, kwana daya bayan tashin hankalin da aka yi a ofishin jakadancin.
Kakakin ma’akatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace, “tashin hankali ba shine hanyar da ta dace ta maida martani ga fadin albarkacin baki ba, muna goyon bayan ‘yancin al’umma a ko’ina, na bayyana ra’ayoyi da kuma gudanarda zanga zangar lumana. Ta kara da cewa, “Muna sanar da gwamnatin kasar Turkiya damuwarmu da kakkausan lafazi.
Saneta John MacCain na jam’iyar Republican, shugaban kwamitin ayyukan soji na majalisa, yace yana son ganin an dauki mataki mai tsauri.
Ya shaidawa wani shirin tashar talabijin ta MSNBC da aka yayata jiya alhamis cewa, “Ya kamata mu kori jakadensu daga Amurka”.
Ofishin jakadancin ya dora alhakin tashin hankalin kan kungiyoyi dake da alaka da jam’iyar PKK, ta kasar Turkiya da cewa, sun tunzura Amurkawa ‘yan asalin kasar Turkiya da suka taru domin yiwa Erdogan gaisuwa.
Facebook Forum