A yau Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki nadin mai bincike na musamman da aka yi don ya binciki ko akwai wata alaka tsakani wadanda suka yi masa campaign da Rasha a zaben da aka yi cikin shekarar da ta gabata, yana kiran matakin na “bita da kullin siyasa na tarihi da aka taba gani a Amurka.
A wasu sakonni da ya rubuta a shafinsa na twitter da safiyar yau, Trump yayi korafin cewa ba a taba cewa za a nada wani mai bincike na musamman don ya binciki “duk miyagun abubuwan da aka tabka a lokacin yakin neman zaben abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat ba, wato tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da kuma gwamnatin shugaba Obama da ta shude.
Trump na maida murtani ne akan nadin Robert Mueller, tsohon shugaban hukumar binciken tarayyar da akayi jiya Laraba, don yayi bincike akan yiwuwar wata alaka tsakanin makarabbansa da jami’an Rasha a zaben, don ba Trump damar samun nasara.
Mr. Mueller ya riga ya fara aikin sa, yayinda hukumar binciken FBI da kwamitin binciken bayanan sirri a majalissar dokoki da ta wakilai sun riga sun fara nasu binciken akan yiwuwar katsalandan Rasha a zaben.
Facebook Forum