Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kai Hari Yankin Jabalia Na Zirin Gaza


Jabalia a arewacin zirin Gaza
Jabalia a arewacin zirin Gaza

Sojojin Isra'ila sun kutsawa cikin Jabalia da ke arewacin Gaza a ranar Talata, inda suka kai farmaki kan wani asibiti da lalata wuraren zama da tankokin yaki da bama-bamai ta sama, kamar yadda mazauna yankin suka ce, yayin da jiragen na Isra'ila suka kashe akalla mutum 5 a Rafah da ke kudancin kasar

WASHINGTON, D. C. - Hare-haren da Isra'ila ta kai lokaci guda a yankunan arewaci da kudancin zirin Gaza a wannan watan ya haifar da wasu sabbin ‘yan gudun hijira na dubban daruruwan jama'a da ke kauracewa gidajensu, tare da takaita kwararar kayan agaji, lamarin da ke kara assasa barazanar yunwa.

Jabalia , arewacin zirin Gaza
Jabalia , arewacin zirin Gaza

A Jabalia, wani sansani na ‘yan gudun hijirar da aka gina wa fararen hula da suka rasa matsugunansu tun shekaru 75 da suka gabata, sojojin Isra’ila sun yi amfani da motocin rusa gidaje wajen ruguza shaguna da kadarori da ke kusa da kasuwar yankin, a cewar mazauna yankin, a wani farmakin da sojoji suka fara kusan makonni biyu da suka gabata.

Isra'ila ta ce ta koma sansanin, inda ta yi ikirarin tarwatsa kungiyar Hamas a watannin da suka gabata, domin hana kungiyar da ke iko da Gaza sake haduwa.

Sansanin 'yan gudun hijira a Jabalia
Sansanin 'yan gudun hijira a Jabalia

A ci gaba da gudanar da ayyukanta bayan kwana guda, sojojin Isra'ila sun ce sun tarwatsa "kimanin hare-haren ta'addanci 70" a duk fadin zirin Gaza, ciki har da ma'aikatun soji, wuraren ajiyar makamai, da harba makamai masu linzami da kuma wuraren da ake kallo.

Likitocin Falasdinawa sun ce makami mai linzami da Isra'ila ta harba a sashen kula da gaggawa na asibitin Kamal Adwan na Jabalia, ya janyo lamarin da ya sa ma'aikatan suka firgita suka kuma garzaya da marasa lafiya a kan gadajen asibiti da shimfidar gado zuwa titin da ke waje.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG