Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya Yi Watsi Da Sukar Da Ake Masa A Gida Da Waje Kan Rashin Takamaiman Shiri Kan Gaza


Israel Remembrance Day
Israel Remembrance Day

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ranar Laraba ya yi watsi da sukarsa da ake yi cewa ba ya shirin fuskantar dahir a zirin Gaza bayan yaki, yana mai cewa ba zai taba yiwuwa a shirya wani yanayi a yankin Falasdinawa da ke fama da rikici ba har sai an fatattaki Hamas.

WASHINGTON, D. C. - Netanyahu na fuskantar karin matsin lamba daga masu suka a cikin gida da kuma aminai a ketare, musamman Amurka, kan bukatar gabatar da wani shiri na mulki, tsaro da sake gina Gaza.

Ya yi nuni da cewa Isra'ila na neman ci gaba da gudanar da harkokin tsaro bisa yadda hali ya yi, tare da yin watsi da bukatar bayar da dama ga hukumar Falasdinu da duniya ta amince da ita ta taka rawa a tsarin. Wannan matsayi ya sha bamban da hankoron gwamnatin Biden ta ta kallafa ranta a kai, wadda ke son a kafa gwamnatin Falasdinu a Gaza da Yammacin Kogin Jordan da Isira’ila ta mamaye a matsayin sharar fagen shirin kafa kasar Falasdinu.

Muhawara kan makomar Gaza bayan yakin na zuwa ne a daidai lokacin da fada ya sake barkewa a wuraren da Isra'ila ta kai hari a farkon yakin da ta ce suna karkashin ikonta, da kuma birnin Rafah da ke kudancin Gaza, lamarin da ya sa dubban daruruwan mutane tserewa.

Ga Falasdinawa, wannan gudun hijirar na sake sabunta tunanin korar jama'a daga kasar Isra'ila a yakin da ya dabaibaye kasar a shekara ta 1948. Falasdinawa a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Laraba suka yi bikin cika shekaru 76 na wannan lamari.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG