Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 27 Sun Mutu A Gaza Yayin Da Shugabannin Isra’ila Ke Takaddama Kan Wanda Zai Mulki Gaza


Wani yankin Falasdinawa
Wani yankin Falasdinawa

Hakan na faruwa ne yayin da Benny Gantz yake barazanar ajiye aikinsa na mamba a kwamitin yaki idan Isra'ila ba ta sauya yadda take tafiyar da yakin na Gaza ba.

Wani harin sama da Isra'ila ta kai Gaza ya halaka mutum 27 akasari mata da kananan yara, sannan kuma fada da Hamas ya barke a arewacin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da shugabannin Isra'ila ke samun rarrabuwar kawuna kan wanda ya kamata ya mulki Gaza bayan yakin.

Firaminista Benjamin Netanyahu na fuskantar suka daga sauran mambobin majalisar ministocinsa na yakin, tare da babban abokin hamayyar siyasa Benny Gantz wanda ya yi barazanar ficewa daga gwamnati idan ba a samar da wani shiri ba nan da ranar 8 ga watan Yuni ko kuma ya yi murabus.

Ficewar tasa dai za ta bar Netanyahu ya dogara ga kawaye masu tsattsauran ra'ayi wadanda ke goyon bayan mamaye Gaza da soji da kuma sake gina matsugunan Yahudawa a can.

Mai ba Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, ya gana da Netanyahu, inda suka tattauna wani gagarumin shirin Amurka da Saudiyya na amincewa da Isra'ila da kuma taimakawa gwamnatin Falasdinawan don kama mulkin Gaza, domin samun hanyar basu kasar kan su.

Ofishin Netanyahu a cikin wata sanarwa ya ce sun mayar da hankali ne kan farmakin da sojojin Isra'ila ke kai wa a kudancin birnin Rafah na Gaza, da taimakon jin kai da kuma mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG