Kimanin alhazai 300 ne na ayarin farkon alhazan Nijer wanijirgin kasar Saudia ya sauka da su a filin jirgin saman Niamey ko Yamai a wajen karfe 8 da minti 20 na daren Larabaagogon Nijer.
Galibin alhazan sun iso ne cikin alamar gajiya yayinda wasu a fili ake ganin raunin da suka ji wasun kuma da jami’an kwana kwana suka sauko su daga jirgin sannan aka dorasu kan kekunan guragu zuwa dakin da aka kebe domin su.
Shugaban kasar Nijer ISUHU MAHAMADU ya yi tattaki zuwa filin jirgin saman domin tarben alhazan.
Tuni dai gwamnati tayi tanadin wuraren musamman a asibitocin kasar domin kula da lafiyar wadanda turmitststin na MINA ya jikkata inji MANU AGHALI ministan kiwon lahiyar al’uma.
Ana sa ran fara jirgilar sauran alhazan na Nijer zuwa gida daga ranar 12 da watan nan.
Ga karin bayani.