Jam’iyyar tsohon shugaban kasar Yamal Ali Abdullah Saleh da kungiyar ‘yan Shi’ar Houthi a kasar sun amince da tayin Majalisar Dinkin Duniya na tsara shirin zaman lafiya da zai kawo karshen tashin hankalin da ake ta zubar da jinin jama’ar kasar.
Dukkanin bangarorin masu nasaba da juna sun fada jiya Laraba sun sanar da Babban Sakataren Majalisa Dinkin Duniya Ban Ki-moon game da bukatar zaman tattaunawar sulhu da juna. Dukkansu ‘yan kungiyar ta Houthi da jam’iyyar Saleh ta General People’s Congress sun aika wasikunsu ga majalisar da shirin shiga
sulhun tare da cewa zasu sa kansu haikan wajen ganin dorewar zaman lafiya bisa tsare-tsare guda bakwai da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a taron da aka yi a Oman watan da ya gabata.
Shugaban kasar Yamal Abdu Rabbu Mansour Hadi ya bukaci mayakan ‘yan Houthi da su fice daga yankin da suka kwace tun fiye da shekara daya. Matukar dai suna son gwamnatinsa tayi wannan zaman tattaunawar sulhun na Majalisar Dinkin Duniya.