Ya fadi haka ne ga manyan kwamandojin juyin juya halin kasar jiya Laraba a Taheran.
Khamenei yace, tattaunawar kai tsaye tsakaninsu da Amurka dama ce ta shigewa jamhuriyar ta Mususlunci.
Duk da yake ya goyi bayan yarjejeniyar da aka kulla ta shirin Nukiliyar kasar, amma bai fito ya sanar a bainar jama’a ba. Yarjejeniyar da kasashen Amurka, Jamus, Faransa, Birtaniya, China da suka kulla kuma ta daidaita kai ruwa ranar da aka fi shekaru 10 ana yi.
‘Yan ra’ayin rikau sun zargi gwamnatin Shugaban Iran Hassan Rouhani da neman kulla kawance da Amurka. Su kansu wasu ‘yan majalisar dokokin Iran masu zafin ra’ayi sun yi barazanar tsige ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif sakamakon yin hannu da Obama watan da ya gabata a New York.