Shugaba Trump, ya caccaki abinda yake kallo a zaman kokarin "dadadawa" ta wajen sassauta dokar farko da ya kafa wacce ta hana rukunin mutane daga wasu kasashe da galibin al'umarsu musulmi ne zuwa Amurka.
Wannan ya biyo bayan wasu rubuce rubucen da yayi a Twitter a farkon jiya, yana aza laifin "sassauta" dokarsa ta farko a kan ma'aikatar shari'ar Amurka, wacce ya sakawa hannu, bayan dokar farkon da ya kafa ta sha kaye a kotu.
Dokar ta farko ta haramatawa mutane daga kasashen Iraqi, da Iran, da Syria, da Libya, da Yemel, da Somalia, da Sudan shigowa Amurka na tsawon wata uku, sannan ta jingine karbar 'yan gudun hijira daga kasar Syria har sai illa masha'Allah, in ban da mabiya addinan 'yan tsiraru daga wannan kasa.
Amma kwaskwarimar da aka yiwa dokar ta fidda Iraqi daga jerin kasashen farko, sannan ta rage haramcin da aka yiwa 'yan gudun hijira daga Syria zuwa kwanaki 120, aka kuma cire batun addinin mutum daga ciki.
Facebook Forum