Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a yau Litinin cewa yana son Kotun Kolin Amurka tayi sauri ta maido da dokar nan da ta haramta wa mutanen wasu kasashe shidda na Musulmi iznin shigowa Amurka.
A cikin jerin sakkoni birjit da ya aika zuwa dandalinsa na twitter, Trump ya caccaki ma’aikatarsa ta shara’a da ya zarge ta da aika abinda ya kira “bayani mai rauni da ya dace da siyasa” zuwa ga Kotun Kolin, dangane da kokarin da yake na hanawa ‘yan kasashen Iran, Syria, Libya, Sudan, Yemen da Somalia shigowa Amurka.
Yace kamata yayi ace ma’aikatar ta aika da tsarin dokar na farko wanda har ila yau ya kunshi Iraq.
Sai dai izuwa yanzu kotuna da yawa na Amurka sun toshe yunkurin, sun hana aiwatarda dokar hanin da ake so yiwa ‘yan wadanan kasashen shidda, inda kotunan suka nuna cewa kalaman dake fitowa daga bakin Trump gameda alakar Musulunci da akidar ta’addanci, da kuma maganar da ya taba yi a lokacin yakin neman zabensa gameda bukatar toshewa Musulmi hanyar shigowa Amurka duk sun sabawa kundin tsarin mulkin Amurka din.
Facebook Forum