Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Birtaniya Sun San Sunayen Mutane Ukun da Suka Kai Harin Ta'adanci


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May
Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

Sanadiyar binciken da suka yi da kuma katunan shaida da suka gano hukumomin tsaron Birtaniya sun bada tabbacin sanin sunayen mutanen nan uku da suka kai hari ranar Asabar da ta gabata.

Frayim-ministar Biritaniya, Theresa May tace yanzu hukuma ta san sunayen mutanen nan guda ukku da suka kai hari akan gadar birnin London shekaranjiya Assabar, inda suka hallaka mutane 7, suka raunana wasu fiyeda 50.

Frayim-ministar tace za’a sako sunayen nasu “da zaran lokacin yin haka ya yi”, har ta kara da cewa an kama karin wasu mutane 11 da ake jin kila suna da hannu a cikin ta’asar.

Haka kuma P-M din tace ‘yansanda na ci gaba da kokarin tantance sunayen mutanen da abin ya shafa, wadanda tace sun hada da mutanen kasashe daban-daban.

Yau Litinin ma ‘yansanda sun ci gaba da gudanarda bincike kuma, inda suka cafke karin mutane a lokacinda suka kai samame a unguwannin Newham da Barking.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG