A Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta jajirce wajen cika alkawurran da ta yi ma kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) na hana yajin aiki, samar da shirye-shiryen karatu ba tare da katsewa ba, da kuma inganta kudade na cibiyoyin ilimi.
Shugaban ya yi wannan alkawarin ne a ranar Talata a Abuja yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar addinai ta Najeriya NIREC.
Shugaban ya yaba wa shugabannin NIREC da suka taimaka wajen sasanta shiga yajin aikin da ASUU ta kwashe shekara guda ta na yi tare da tuntubar jam’iyyu. Shugaban ya ce babu wata al’umma da ke fatan alheri da cigaba da za ta yi watsi da tsarinta na ilimi.
Shugaba Buhari ya bukaci NIREC da cewa a tattaunawar da za ta cigaba da yi da mambobin kungiyar ASUU, ta fada musu cewa gwamnati na girmama su da kuma hidimar da suke yi wa al’umma sosai.
“A nasu bangaren, ina kara jan hankalin ASUU da su ci gaba da hada kai da mu wajen nemo mafita kan kalubalen da ke gabanmu.
''An kuma samar da kudade don inganta ababen more rayuwa a jami'o'in gwamnati da dama kuma da da yawa daga cikinsu sun fara cin moriyarsu wajen inganta ayyukansu.