Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nada Pantami A Matsayin Farfesan Koyar Da dabarun Tsaron Yanar Gizo Bai Saba Ka’ida Ba - ASUU


Kungiyar ASUU
Kungiyar ASUU

Wani kwamitin bincike da kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya wato ASUU ta kafa a jami’ar fasahar Owerri ta jihar Imo, ya ce an bi tsarin da ya dace wajen bai wa dakta Isa Ali Pantami matsayin farfesa a fannin dabarun tsare yan kasa a yanar gizo.

A cewar kwamitin ASUU, majalisar gudanarwa jami’ar FUTO ta bi tsari da dokokin da suka kafa jami’o’in Najeriya wajen bai wa ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, Isa Pantami matsayin farfesa a fannin tsaron kafar Intanet ga yan kasa.

A cikin rahoton da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, kwamitin mai wakilai biyar ya ce ya tattauna da wasu masu ruwa da tsaki da suka hada da shugaban jami’ar da kuma tsohon shugaban kwamitin malaman jami’o’i da dai sauransu kuma basu sami inda aka aikata ba daidai ba a lamari na Pantami.

Bayan gudanar da binciken, kwamitin wanda aka kaddamar a ranar 22 ga watan Satumban shekarar 2021, ya bukaci mahukuntan jami’o’in da su dauki matakin da ya dace ta fuskan shari’a kan wadanda suka yi yunkurin bata wa jami’ar suna da rage kimarta a bainar al’umma da gangan.

Tawagan kwamitin binciken wanda ya hada da Farfesa M. S. Nwakaudu, G.A. Anyanwu, CE Orji, OP Onyewuchi da T.I.N Ezejiofor, sun ce sai da aka yi tallar guraben aikin ma’aikatan ilimi da na masu taimaka musu a jami’ar FUTO don maye gurbin mukaman Farfesa, masu karanta rubuce-rubuce, babban malami da ma karamin malami a jaridu biyu a ranar 21 da 22 na Satumbar shekarar 2020 a kai a kai.

Kwamitin ya kara da cewa Pantami ya nemi mukamin na Farfesa a fannin tsaro na Intanet kuma bayan wani nazari aka nada shi a matsayin na wucin gadi, wanda ya karba a rubuce.

Kazalika kwamitin ya ce daga bisani an gabatar da Dakta Isa Pantami a gaban kwamitin tantance ma’aikatan ilimi da ci gaban ilimin Farfesa wato ASAPC-Professorial da aka gudanar a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2021.

"Kwamitin ASAPC-Professorial ya tattauna batun kuma ya ba da shawarar amincewa da matakin nada Pantami Da majalisar jami’ar FUTO ta yi."

Ita kuwa majalisar a zamanta da ta gudanar a ranar 18 ga Maris na shekarar 2021 ta amince da matakin shari’ar farko da aka shigar kan nada dakta Isa Ibrahim a matsayin Farfesa a harkar tsaro ta Intanet.

Biyo bayan amincewa da shari'ar, an aika da rubuce-rubucen Dakta Isa Pantami da ayyukansa masu inganci don tantancewa ga mutanen da ke aikin tantancewa na wajen jami’ar.

Wasu masu aikin tantancewa na waje ma sun dawo da sakamakon amincewa da ya yi daidai da na kwamitocin biyu da suka yi aikin tantancewar a baya, yayin da kuma majalisar jami’ar FUTO a taronta na ranar 20 ga watan Agustar shekarar 2021 ta amince da nadin sa a matsayin farfesa na tsaron kafar intanet inda aka ba shi mukamin bayan nadin da majalisar gudanarwa ta FUTO ta yi.

Duk kokarin ji ta bakin ministan sadarwar da tattling arzikin fasahar zamani kan annan lamari a lokacin hada wannan labran da ya ci tura.

XS
SM
MD
LG