Ko da ya ke malaman sun ce idan gwamnati ba ta cika alkawuranta zuwa karshen watan Janairun badi ba, to za su sake tsunduma ciki wani yajin aikin na sai baba ta gani.
Sanarwar dai na zuwa ne bayan ganawar da ASUU ta yi da gwamnatin tarrayya, inda bangaren gwamnati ya amince zai biya malaman albashinsu tun daga watan Fabrairu na bana zuwa watan Yuni da tsohuwar manhajar da aka saba biyansu da ita.
Hakazalika gwamnati ta amince da kara kudin alawus na malaman daga Naira biliyan 30 zuwa Naira biliyan 35 sannan kudin gyara Jami'o'i kuma daga Naira biliyan 20 zuwa Naira biliyan 25.
Farfesa Muntaqa Usman, na Jami'ar Ahmadu Bello, Shi ne mai yi wa Kungiyar fasarrar manufofinsu a hausa, ya yi bayanin cewa akwai batun gyara dokoki na mallakar jihohi da za a kai gaban majalisar dokokin kasa. Farfesa Usman ya kara da cewa, za a kafa kwamitin da zai rika kai ziyara jami'o'in kasar akai-akai, sannan za a ci gaba da tattaunawa da bangaren gwamnati akan yadda za a samu ci gaba a dukkanin bukatun kungiyar ta ASUU.
To sai dai mai nazari a al'amuran yau da kullum Komred Isa Tijjani, ya yi tsokaci akan matakin da gwamnati ta dauka, inda ya ke ganin kamar ba za ta iya cika alkawuran ba saboda karyewar da tattalin arziki kasar ya yi a sakamakon annobar coronavirus.
Wannan yajin aikin shi ne mafi tsawo a tarihin kasar. Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a jami'o'i a daidai lokacin da malaman za su koma karatu a yanayi na bazata na samun cikakkun kayan aiki.
Saurari rahoton Medina Dauda Daga Abuja.