Bayan an kwashe wadanan wattanin a yanzu dai gwamnati ta amince da bukatun Kungiyar Malaman Jami'o'i ta ASUU da ke cewa a dakatar da batun sa mambobinta a manhajar IPPIS inda gwamnati ta ce ta hakura da wasu lamura wadanda suka hada da wajabta biyan Malaman ta IPPIS da kuma kara masu kudin alawus da kudin gyara jami'o'i.
Mai magana da yawun Kungiyar ASUU kuma Malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, farfesa Muntaqa Usman ya ce duk da wannan mataki da aka cimma da Gwamnati, Malaman ba su amince ba tukuna sai sun gana da dukannin malaman jami'o'in sannan su dawo wa Gwamnati da matsayar su.
Ministan ma’aikatar Kwadago Chris Ngige ya bada umurnin cewa hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya ta zauna da manya-manyan shugabanin jami'o'i domin su fito da jaddawalin da za a yi amfani da shi wajen biyan basussukan Malaman, kuma Ngige ya ce gwamnati ta amince a yi amfani da tsohowar manhajar da ake amfani da ita tuntuni domin a biya su albashin da shi.
Amma mai nazari kan al'amuran yau da kulum Komred Isa Tijjani, ya ce yaudara ce kawai gwamnati ta ke yi wa Malaman, ba za ta yi abubuwan da ta ce ba saboda a ganinsa kasa ba ta kudi, basussuka kawai ake ci.
Gwamnati dai ta ce ta amince da kara kudin alawus na Malaman daga Naira biliyan 30 zuwa Naira biliyan 35 sanan kudin gyara jami'o'i daga Naira biliyan 20 zuwa Naira biliyan 25.
A yanzu dai iyaye da dalibai sun zuba ido su ga yadda za ta kaya tsakanin ASUU da Gwamnati da ke shirin yi wa wani bangare na Malaman jami'o'in mai suna CONUA rajista.
Saurara karin bayani cikin sauti: