Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da malaman addini ke bukaci bangarorin biyu su sasanta da juna domin dalibai su koma makaranta.
Batun sanya malaman Jami’o’I akan manhajar IPPIS ta biyan ma’aikata albashi na bai daya da gwamnati ta samar na daga jerin bukatun ‘yayan kungiyar ta ASUU da suka haifar da tankiya tsakanin gwamnati da kungiyar.
Malaman Jami’ar dai na da’awar cewa, manhajar ta gwamnati ta saba da yanayin tafikar da ayyukan Jami’a, don haka suka ki amincewa da ita. To amma amadadinta sun kirkiro wata sabuwa mai lakabin UTAS da suka cE zata tabbatar da tsantseni da kasawa a fefe kan yadda shugabannin Jami’o’in Najeriya ke sarrafa kudaden da suke samu.
Farfesa Mahmud Lawan shine shugaban kungiyar ta ASUU mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Ya kara da cewa a wata zama da suka yi da wakilan gwamnatin, sun amince da manhajar kana suka ce za a gudanar da gwajin inganci akai, a dan haka malaman jami’ar na jiran mataki na gaba da hukumomin zasu dauka.
Baya ga manhajar sarrafa kudaden Jami’a, batun samar da isassun kudaden aiki ga jami’o’in da kayayyakin aikin da suka dace da zamani da kula da walwalar Malaman na cikin dalilan yajin aikin da ‘yan kungiyar ta ASUU keyi tsawan watanni 8, lamarin daya sanya dalibai suka fara kokawa.
Baya ga dalibai, suma malaman addini sun shiga Tsakani ta hanyar kira ga bangarorin biyu suyi sulhu da juna.
A yayin taron masu ruwa da tsaki da al’umar garin wadda reshen Jami’ar Bayero na kungiyar ta ASUU ya shirya a karshen mako, Sheikh Abdulwahab Abdallah guda cikin mashahuran Malaman musulinci a Najeriya ya roki gwamnati da Malaman Jami’ar su kawo karshen wannan takaddama saboda illarta ga makomar rayuwar matasa.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum