Saboda gudun kada shugaba Buhari ya amince da shawarar masu cewa ya manta da bincikar abubuwan da suka faru a baya ya sa kungiyoyin kare hakin bil Adama suka fito suka yi gangami.
Masu gangamin sun nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammad Buhari akan matakin da ya dauka na yakar cin hanci da rashawa da alkawarin hukumtar da duk wadanda bincike ya nuna suna da hannu a wawurar dukiyar kasa.
Kungiyoyin suna adawa da abin da suka kira katsa landan da wasu suk yiwa shirin shugaban musamman kwamitin zaman lafiya a karkashi shugabancin tsohon shugaban mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar..
Daya cikin shugabannin masu gangamin I.G.Wala yace abun da ya kaisu shi ne si isar da sako ga shugaban kasa. Sun kira shugaban kasa kada ya karaya. Ya tabbatar da cewa ya aiwatar da kudurin da ya yi na yaki da cin hanci da rashawa.. Ya cigaba dashi sosai.
Shi shugaban ta bakin kakainsa Femi Adesina ya tabbatar masu da cewa yaki da cin hanci da rashawa yanzu ne ma aka fara.
Amma Dr Yunusa Tanko wakilin kwamitin zaman lafiya yace tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fada masu abubuwan dake tayar masa da hankali. Yana ganin ana zabar wadanda ake so a tuhuma wato za'a kare wasu. Wai Jonathan bai ce kada a hukumta kowa ba amma a yi adalci.
Bisa ga abun da suka ji suka ba shugaban kasa shawara ayi bisa doka da oda a kuma tabbatar da yin adalci.
Ga rahoton Hssan Maina Kaina.