Halayan sojojin na yiwa 'yancin dan Adama a Najeriya karan tsaye.
Kungiyoyin sun bayyana yadda kwana kwanan nan a Makurdi babban birnin jihar Binuwai wasu sojoji suka yi diran mikiya akan wasu fararen hula inda suka azazzalesu da lakada masu dukan tsiya sanadiyar wani rashin fahimta da ya shiga tsakaninsu.
Dan rajin kare hakin bil Adama Kwamred Shehu Sani yace yanzu fa mulkin dimokradiya a keyi. A karkashin mulkin dimokradiya bai kamata hakan ya faru ba saboda tsarin mulki ya bayyana abun da sojoji zasu iya yi da kuma abun da fararen hula zasu iya yi..
Daga lokacin da jama'a suka san 'yancinsu kuma suka san inda zasu je a kare masu hakinsu to irin wannan halin na sojoji dole ya kau.
A wani bangaren kuma kwamandan sojojin Najeriya dake Binuwai Manjo Janar Bamidele Ogunkale ya garzaya gidan gwamnati inda ya baiwa gwamnan Chief Otom hakuri akan aika-aikar sojojinsa.
Shi ma kakakin sojojin Kanar Sani Usman Kukasheka ya sanar cewa akwai matakan da suke dauka yanzu. Yace an zauna an kafa kwamitin bincike kana kwamandansu ya bada hakuri. Duk wani wanda yake da hannu cikin sojojin za'a ladaftar dashi. Yanzu sojojin da suka fita daga bariki ana tsare dasu.
Masana harkokin shari'a na nuna damuwa akan halayen sojojin kasar. Barrister Yakubu Bawa yace tsarin mulkin kasa ya ba kowa martaba. Idan akwai rashin jituwa tsakanin fararen hula da soja su nufi wurin 'yansanda suka kai korafinsu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.