Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ba Zai Amince da Rashin Gaskiya Ba a Daukan Sabbin 'Yansanda


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Yayinda ake shirin daukan sabbin 'yansanda shugaban kasa ya ja kunnen mahukata kada su kuskura su tatsi mutane

Yau Talata shugaba Buhari a Abuja ya ja kunnuwan wadanda zasu dauki karin 'yansanda kada su kuskura su tatsi jama'a ta hanyar neman na goro daga 'yan Najeriya dake neman aik wadanda basu da aikin yi.

Yayinya da yake ganawa da jami'an ma'aikatar dake kula da harkokin 'yansanda a fadarsa ta Aso Villa yace yadda ake karban na goro daga hannun masu son shiga aikin 'yansanda can baya rashin adalci ne kuma shi ba zai yadda da hakan ba.

Wadanda aka dorawa alhakin daukan sabbin 'yan sanda da horas dasu dole ne su kasance mutane masu aiwatar da adalci, su kawar da son zuci da kuma son kai.

Yace dole su tabbatar sun yi adalci wurin daukan sabbin 'yansandan yadda kowa zai ga an yi abun cikin gaskiya.

Daga bisani shugaban kasa ya gargadi babban sifeton 'yansanda Mr. Solomon Arase ya janye jami'an 'yansanda da aka turasu kare wasu ya mayar dasu cikin aikinsu. Ma'ana wadanda suke biya domin 'yansanda su basu kariya a daina nan take.

Shugaban ya gayawa ma'aikatar ta warware matsalar rashin karawa 'yansanda girma a lokacin da yakamata. Ana yawan barin mutane akan matsayi daya su yi shekara da shekaru ba'a kara masu girma ba ba'a kuma basu dalilin yin hakan ba.

XS
SM
MD
LG