Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Zai Kara Yawan 'Yansanda


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

A taron tsaro da yayi da 'yansanda a Abuja shugaba Buhari yayi alkawarin kara yawansu saboda karancin 'yansandan.

Aniyar karin 'yansanda dubu goma ya nuna cewa akwai karancinsu a kasar saboda da ywawa suna kare lafiyar wasu ne maimakon aikin tsaron kasa..

'Yan kalilan ne suka rage da suke aikin kare al'ummar kasar da suka kai miliyan 170.

Shugaban ya kara nanata muradun gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da jawo al'umma kusa da 'yansanda domin aiki tare wanda yin hakan zai dakile miyagun laifuka kamar fasa gidaje da fashi da makami da sace shanu ko mutane don samun kudin fansa.

Shugaban hadin kan Fulani Usman Usman yace akwai yawan baragurbi cikin 'yansanda. Yace idan yara suka yi fada daya ya jiwa dayan rauni sai ka ga dagacin garin da 'yansanda sun hada baki suna tilastawa mahaifin wanda aka kama ya dinga sayar da shanunsa yana bada cin hanci. Sai sun zazzage mutumin su bar shi ba saniya ko daya kana a sako dan.

Bafillacen da ya rasa shanunsa to me kuma ya rage sai shiga halayen banza na karya dokoki. Kamata yayi shugaban kasa ya magance abun.

Masanin harkokin tsaro Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yace irin taron dake da sa hannun fararen hula zai kawo karshen kalubalen tsaro.

Babban sifeton 'yansandan Najeriya Solomon Arase ya tura motocin sintiri 555 domin su maye gurbin sansan da aka janye shingayen sojoji domin magance wadanda suke labewa da tsaron suna cin zarafin wadanda basu da tsaro.

Na rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG