Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Rage Wa Yara Talauci A Duniya Ya Gamu Da Matsala babba


Asusun UNICEF yace tashin gwauron zabin farashin abinci da sauyin yanayi su da rage kasafin kudi a kasashe su na kawo tafiyar hawainiya a kokarin kawar da talauci a tsakanin yara,

Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, yace rage kasafin kudi a kasashe, da tashin gwauron zabin farashin abinci da kuma sauyin yanayi su na kawo tafiyar hawainiya a kokarin kawar da talauci a tsakanin yara, yayin da bambancin halin rayuwa ke karuwa a tsakanin yara na kasashe masu arziki da matalauta.

A cikin wani rahoton da ya bayar yau talata, asusun na UNICEF yace koma-bayan tattalin arzikin duniya ya haddasa rage yawan kudaden agajin da wasu kasashe ke bayarwa a cikin kasafce-kasafcensu.

Babban darektan asusun, Anthony Lake, yace yara marasa galihu sune suka fi shan tasku a saboda wannan lamarin. Yace ana kara ganin shaidar cewa irin nasarorin da asusun UNICEF yake samu a wasu muhimman fannoni ya bambanta, ciki harda batun rage mace-macen yara kanana.

Rahoton ya bayar da shawarar cewa mayarda hankali kan bukatun yara marasa galihu na iya zamowa hanya mafi a’ala ta rage yawan mace-macen yaran.

Wannan rahoto na asusun UNICEF yana zuwa ne dab da taron kolin duniya da za a yi domin nazarin ci gaban da asusun ya samu wajen cimma gurorin da aka kafa shekaru 10 da suka shige na rage yawan mace-macen yara da rabi idan an kwatanta da adadin mace-mace na shekarar 1990.

XS
SM
MD
LG