Wata kungiyar yaki da talauci mai hedkwata a kasar Afirka ta Kudu ta ce yunwa tana sanya kasashe matalauta da masu tasowa su na yin hasarar dala miliyan dubu 450 a kowace shekara wajen kula da lafiya da kuma rashin iya zuwa aiki na masu fama da yunwar.
Wannan sabon rahoto na Kungiyar ActionAid ya nazarci yunkurin yaki da yunwa a kasashe 28 masu tasowa. Ta ce kasashe 20 daga cikin 28 da ta nazarta ba zasu iya cimma gurin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a 2000 na rage yawan masu fama da yunwa da rabi nan da shekarar 2015 ba.
Rahoton yace kasashen da suke kashin baya a kokarin rage yunwa sune Lesotho da Pakistan da Saliyo da Burundi da kuma Kwango ta Kinshasa.
Kasashen da suke sama a kokarin yakar yunwa sune Brazil da China da Ghana da Malawi da kuma Vietnam. Kungiyar ActionAid ta ce wadannan kasashe biyar sun tashi haikan wajen zuba jari a kananan gonaki da shirye-shirye kamar samar da ayyukan yi na gwamnati da kuma ba ‘yan makaranta abincin rana kyauta a makarantunsu.
Har ila yau kuma, ActionAid ta auna kokarin kasashe masu arziki su 23 wajen tallafawa yaki da yunwa a duniya. Ta ce kasashen da suka fi taimakawa su ne Luxembourg da Faransa da Spain da Sweden da kuma Canada. Kasashe masu arziki dake baya a kokarin tallafawa yaki da yunwa sune Austria da New Zealand da Greece da Koriya ta Kudu da kuma Portugal.