Wani sabon nazari ya gano cewa yaran dake zaune a gidajen da akwai rima ko damshi-damshin ruwa sun fi fuskantar kasadar kamuwa da mura ko cuce-cucen numfashi.
Masu binciken da suka shafe shekaru shida su na sanya idanu a kan wasu yara dubu daya da dari shida a kasar Finland, sun gano cewa daga cikin wadannan yara, wadanda ke zaune a cikin gidajen dake da rima ko kuma ruwa yana kwanciya ciki, sun fi kamuwa da kumburin hanci ko kuma jijiyoyin cikinsa.
Alamun ciwon na kumburin hanci ko jijiyoyin cikinsa, sun hada da toshewar hanci, atishawa, da yoyon majina wadanda ake samu a dalilin shakar kura, ko wasu abubuwa a cikin iska.
A wannan nazarin da aka wallafa cikin mujallar Cibiyar Nazarin yaduwar Cututtuka ta Amurka, kashi 16 cikin 100 na yaran da iyayensu suka ce akwai damshi-damshi a cikin gidajensu, sun kamu da ciwon kumburin hanci. A tsawon lokacin wannan nazarin, kasa da kashi 12 cikin 100 na yaran da iyayensu suka ce babu wani damshi-damshi cikin gidajensu ne kawai suka kamu da irin wannan ciwo.
Masana sun ce rima da damshi-damshi a cikin gida yana kara kasadar yara ta kamuwa da cuce-cucen numfashi. Yaran da iyayensu suka bayar da rahoton rima ko damshi-damshi cikin gidajensu, su na fuskantar karuwar kashi 55 cikin 100 a kasadarsu ta kamuwa da wani ciwo na numfashi, idan an kwatanta da masu zama cikin gidajen da babu irin wannan.