Hukumomi a kasar Guinea-Conakry sun haramta yin zanga-zanga a titunan kasar a bayan da aka kashe mutum guda, aka raunata wasu akalla hamsin a fadan da aka gwabza tsakanin magoya bayan ‘yan takara masu hamayya da juna a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da za a yi.
Magoya bayan ‘yan takarar biyu, Cellou Dalein Diallo da Alpha Conde, sun ba hammata iska a titunan birnin Conakry a ranakun asabar da lahadi. Sai da ‘yan sanda da dakaru suka shiga tsakani domin kawo karshen fada a tsakanin sassa masu jifa da duwatsu da kai farmaki kan motoci.
Kowannensu yana zargin daya bangaren da laifin tayar da wannan fada.
Tankiyar siyasa ta kara zafi a kasar Guinea tun ranar alhamis, a lokacin da aka yanke hukumcin daurin shekara guda-guda a kan wasu manyan jami’an zabe na kasar a saboda zarginsu da laifin aikata magudi a zagayen farko na zaben shugaban kasa a watan Yuni.
Diallo, wanda ya taba rike mukamin firayim minista, shi ya zo na daya a zagayen farko da kashi 44 cikin 100 na kuri’un. Conde, wanda ya jima yana dan hamayya, ya zo na biyu da kashi 18 cikin 100. Mutanen biyu zasu kara da juna a zaben fitar da gwani ranar lahadi mai zuwa.