Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya ce duk wata muzahara da almajiran El-zakzaky suka shirya za su gudanar tamkar aikin ta’addanci ne.
Adamu a sanarwa da kakakin rundunar, Frank Mba, ya fitar, ya ce rundunar na sane da shirin ‘yan Shi’a na kungiyar IMN na fitowa don gudanar da gagarumar zanga-zanga da ka iya ta da fitina a yankunan Najeriya.
Don haka rundunar za ta tunkari duk mai shirin wannan zanga-zanga a matsayin mai aikin ta’addanci don an haramta kungiyar ta almajiran El-zazzaky IMN a takaice.
Daya daga masu magana a madadin almajiran na El-zazzaky, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya ce za su fito muzahara a ranar Talatar nan don ranar Ashura da ‘yan Shi’a kan yi juyayi a duk shekara kenan.
Rundunar dai ta ‘yan sanda ta bukaci iyaye su hana ‘ya’yansu aukawa kungiyoyin ta da hankali ko zanga-zanga marar bin ka’ida.
Rahotanni na bayyana cewa almajiran El-zakzaky ka iya amfani da damar ta gagarumar zanga-zanga don tilasta gwamnati ta saki shugabansu da ake gudanar da shari’arsa a babbar kotun Kaduna.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum