Wani tsohon dan Majalisar Wakilan Najeriya, mai suna Aminu sani Jaji da yake ziyara a nan Amurka, ya ce sata da garkuwa da mutane da kashe kashe da kuma satar shanu, su ne manyan kalubaloli da ke addabar Najeriya, musamman al’ummar yankin arewacin kasar. Ya ce duk da kokarin da wasu gwamnatocin jihohi suka yi da sauran aiki.
Aminu Sani Jaji ya ce bindiga da bindiga ba zai magance wannan matsala ta tsaro a rewacin Najeriya ba, don haka yakamata a fito da wani tsari da zai tantance ayyukan da gwamnatocin suke yi. Ya kuma bada shawarar zama da masu aikata danyen aikin domin fahimtar juna saboda yin hakan zai taimaka.
Hon. Jaji ya ce akwai wasu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu ‘yan bindigan suna neman su ajiye makamansu saboda suna so su dawo cikin al’umma su fara wata sabuwar rayuwa, don haka irin wannan tsari zai taimaka wurin tattaunawa da su domin su ajiye makaman nasu.
Ya ce dole ne gwamnatin tarayya ta shigo da wannan tsari yanda za a yi aiki bai daya, in ba haka ba za a samu sauki a wata jiha amma kuma rikicin ya koma wata jiha. Idan gwamnatin tarayya ta shiga cikin wannan aiki za a samu maslaha.
Hon. Aminu Sani Jaji ya yi wadannan bayanai ne a wata hira da Muryar Amurka ga kuma hirar:
Facebook Forum