'Yan Shi'a sun yi muzahara da nufin nuna bacin rai akan kashe-kashen rayukan da ake fuskanta a duniya, misalin abubuwan da suka faru a bayan nan tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, da dai sauransu.
Sabanin yadda wasu ke daukar ranar Ashura a matsayin ranar cika ciki, mabiya mazabar shi’a na kallon ranar ta 10 ga watan Muharam, a matsayin ranar nuna bacin rai akan muzgunawar da bayin Allah ke fuskanta. Misalin kisan da aka yiwa Imam Hussein, da makarrabansa, ba tare da aikata laifin komai ba, inji Sheik Salissou Ahmed Lazaret jagoran ‘yan Shi’a a Nijar.
Tashe tashen hankulan da ake fuskanta a kasashen Duniya, wani al’amari da ‘yan shi’a suka ce yana da nasaba, da rashin mutunta hakki, saboda haka suka kudiri aniyar yakar wannan haramtaciyar halayya.
Halin da jagoran ‘yan shi’a a Najeriya Sheik Ibrahim El-Zakzaky ke ciki na daga cikin abubuwan da wannan zama ya yi tur da su.
Tsarin kasafta albarkatun karkashin kasar da Allah ya horewa Nijar wani abu ne da shugabannin Shi’a suka ce suna da damuwa a kansa.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum