Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar A Yi Nazari Sosai Kafin A Dauki Jami'in Tsaro Aiki - Inji Otaki Osana


Ganin yadda kwararru ke bayani cewa akwai alaka tsakanin ta'addanci da batun sauya dabi'a, Farfesa Otaki Osana Alananan, na Jami'ar Abuja ya ce a rika bin diddigin irin mutanen da za a dauka aikin jami'in tsaron kasa.

Sufeto Janar na 'yansandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ce an ceto 'yan Najeriya 837 wadanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su sannan an samu nasarar kwato makamai 1,356 a hare haren da jami'an tsaro suka kai a fadin kasar. Hakazalika an kama harsasai dubu 21,300.

Kwararre a harkar tsaro na kasa da kasa kuma shugaban kamfanin tsaro na BICON Securities, Kabir Adamu, ya ce abinda ya kamata shi ne a yi kokarin gurfanar da masu laifi a gaban kotu saboda a hukunta su akan laifukan da suka aikata, domin yin haka zai yi nuni ga wadanda ke da niyar shiga wanan hali na ta'addanci cewa ba aiki ne mai kyau ba, saboda haka za su ji tsoron yi, abu na biyu kuma a ja su kusa da jiki domin a yi kokarin sauya masu dabi'a domin an lura yawancin su ba su da ilimin addini ko na boko, saboda haka nuna masu kula yana iya sauya tunanin su.

Ganin yadda kwararru ke bayanin cewa akwai alaka tsakanin ta'addanci da batun sauya dabi'a, Farfesa Otaki Osana Alananan, na Jami'ar Abuja ya ce a rika bin diddigin irin mutanen da za a dauka a aikin jami'in tsaron kasa, ba kawai a debi kowane irin mutane ba. Ya bada shawara akan a koma salon daukar aiki da ake yi a baya, inda ake sanin asalin mutum kafin a dauke shi aikin jami'in tsaro, ya ce yin haka zai rage cin hanci da rashawa da ya yi katutu a jami'an tsaron kasar.

Shi ma Tsohon Shugaban Hukumar Wayar da kan al'umma ta kasa wato NOA, dakta Mike Omeri, ya ce akwai rashin shugabanci ingantacce saboda haka dole ne a wahala kafin a ja hankalin mutane su rika hadin kai wajen mu'amalar da zata kawo zamantakewa mai ma'ana saboda a rinka fahimtar juna koda a wajen musayar ra'ayi ne.

Dakta Omeri yace da shi da wasu 'yan'uwansa suna kokarin fito da tsarin da zai taimakawa shugabanni da al'umma baki daya wajen gyara dabi'unsu.

Ya kuma yi fatan yin hakan zai taimaka wajen kawar da kyama da rashin jituwa a tsakanin al'umma.

Akwai Bukatar A Yi Nazari Sosai Kafin A Dauki Jami'in Tsaro Aiki - Inji Otaki Osana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00



Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG