Wasu manyan wakilan majalisar dokokin Amurka biyu sun yi kira ga gwamnatin Obama ta goyi bayan a kafa gwamnatin wucin gadi a gabashin Libya,yayinda kiraye kirayen neman shugaban Libya Moammar Gadhafi ya sauka yake kara karuwa,kuma wasu Karin garuruwa suka fada hanun ‘yan adawa a kasar.
Lahadi ‘yan adawa suka bada sanarwar sun kafa “Majalisar kasa” a gabashin kasar,da suka kwace daga hanun sojoji dake biyayya ga shugaba Moammar Kadhafi.
Daga yammacin Libya,sojojin ‘yan adawa sun kama Zawiya,wani birni mai muhimmanci, mai tazarar kilomita 50 daga Tripoli,babban birnin kasar.
Lahadi, Mallam Gadhafi ya yi watsi da ‘yan adawa,yana cewa ‘yan tsiraru ne da sojojinsa suka yi wa zobe. A hira ta tashar talabijin ta Serbia da ake kira “PINK”,shugaban Libyan ya yi Allah wadai da takunkuminda kwamitin sulhu ya azawa kasar a karshen mako, dangane da mummunar farmakinda gwamnati ta kai wa masu zanga zanga zanga.
Azamansa na karshen mako,Kwamitin ya yarda ya mika Libya ga kotun hukunta manyan laifuffukan yaki domin ta binciki ko an aikata laifuffukan keta haddin bil’adama.
Senatocin Amurka biyu,John McCain da Joseph Lieberman, sun ce gwamnatin Obama ta kafa dokar hana shawagin jiragen yaki a wani bangaren Libya,domin hana Moammar Gadhafi daga kai wa jama’ar kasar farmaki da jiragen yaki. Haka kuma sun ce tilas Amurka ta goyi bayan ‘yan hamayyar Libya.
Da yake magana ta cikin shirin “Meet the Press” na tashar talabijin ta NBC,Senata McCain yace “tilas Amurka ta goyi bayan gwamnatin wucin gadi,watakil a wajajen gabashin kasar Libya,watakil a Bengazi. Tilas mu fito karara mu nuna zamu tallafawa “gwamnatin wucin gadin”.
Ahalin yanzu kuma,’Yansanda a China sun fito da karfinsu ranar lahadi domin su tinkari wani masu amsa tayin sako ta Internet daga ketare, dake kiran jama’ar kasar suyi koyi da masu zanga zangar rajin Demokuradiyya dake ratsa gabas ta tsakiya,da kuma arewacin Afirka.
Senata McCain yace sai tayu China ta kasance daya daga cikin kasashe da zata fuskanci karin guguwar zanga zanga dake kadawa.
“Bana jin wan nan iskar canji zata tsaya a kasashen larabawa da yankin Afrika na Magrhreb kadai ba.Ina ji zai faru ta ko ina a Duniya.Watakil,irin abinda ke faruwa a China da wasu kasashen Duniya.
Kamin tashinta lahadi zuwa taron hukumar kula da hakkin bil’adama ta Majalaisar Dinkin Duniya a Geneva, sakatariyar harkokinn wajen Amurka Hillary Clinton, tace Amurka tana tuntubar ‘yan hamayya a Libya.Duk da haka ta yi gargadin cewa babu tabbas kan al’amura a Libya.