Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai daya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri'ar azawa shugaban Libya takunkumi


Jakaden Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya Mark Lyall Grant da jakadiyar Amurka Susan Rice suna kada kuri'a kan zaman lafiya da kuma tsaro a Afrika
Jakaden Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya Mark Lyall Grant da jakadiyar Amurka Susan Rice suna kada kuri'a kan zaman lafiya da kuma tsaro a Afrika

Bai daya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’a azawa shugaba Moammar Gaddafi na Libya da iyalinsa da manyan murabbaransa takunkunmi dangane da mumunar murkushe masu zanga zangar kin jinin gwamnati, kuma za’a mika wannan batu gaban kotun kasa da kasa dake shari’ar laifuffukan yaki.

Bai daya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’a azawa shugaba Moammar Gaddafi na Libya da iyalinsa da manyan murabbaransa takunkunmi dangane da mumunar murkushe masu zanga zangar kin jinin gwamnati, kuma za’a mika wannan batu gaban kotun kasa da kasa dake shari’ar laifuffukan yaki. Wannan kuduri da aka zartar a jiya asabar ya tanadi hanawa Mr Gaddafi da yayansa maza guda hudu da mace daya da kuma wasu yan uwansa guda goma amfani da kadarorinsu na kasashen waje. Haka kuma an haramtawa dukkansu su goma sha shidda yin tafiye tafiye a wasu kasashe. Wakilan kwamitin sun yarda suke karar gwamnati gaban kotun shari’ar laifuffukan yaki domin binciken yiwuwar laifuffukan da aka aikata wa Bani Adamu. Haka kuma kwamitin ya bukaci nan take magoya bayan Mr Gaddafi su kawo karshen kaiwa masu zanga zangar hare hare. Majalisar Dinkin Duniya tace an kashe fiye da masu zanga zangar dubu daya a Libya. Anan birnin Washington DC kuma, shugaba Barack Obama na Amirka yace Mr Gaddafi yayi hasarar halacin yin mulki a saboda haka yayi murabus nan da nan.

XS
SM
MD
LG