Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasashen Waje Da Yawa Sai Kaura Su Ke Ta Yi Daga Libiya


Daruruwan 'Yan Turkiyya da ke Libiya kenan ke jiran su shiga jirgin ruwa mai suna Orhan Gazi zuwa gida.
Daruruwan 'Yan Turkiyya da ke Libiya kenan ke jiran su shiga jirgin ruwa mai suna Orhan Gazi zuwa gida.

Da Canada da Burtaniya sun tura jiragen sama zuwa, Tripoli, babban birnin kasar Libiya a yau Alhamis, a cibagaba da jan aikin jigilar ‘yan kasashen waje da ake yi daga kasar.

Da Canada da Burtaniya sun tura jiragen sama zuwa, Tripoli, babban birnin kasar Libiya a yau Alhamis, a cibagaba da jan aikin jigilar ‘yan kasashen waje da ake yi daga kasar.

Rashin kyawun yanayi ya tilasta wa wani jirgin da Amurka ta tura dakatawa a filin jirgin Tiripoli duk tsawon dare, wanda ya kawo jinkiri wajen kokarin kwasar Amurkawa zuwa Malta.

Dubun dubatan ‘yan kasashen waje na ta shiga jiragen sama, da na zuwa da ma motoci wani sa’in ma a cunkushe a kokarinsu na kauce wa rudamin day a biyo bayan zanga-zangar kin gwamnati da kuma salon gwamnati na murkushe zanga-zangar.

Wasu jiragen ruwan kasar Turkiyya biyu sun kwashi turkawa wajen 3,000 daga tashar jirgin ruwan Benghazi da ke gabashin kasar ta Libiya a jiya Laraba, a wani abin da Ministan Harkokin wajen Turkiyya ya kira aikin jigila mafi yawa a tarihin Turkiyya. An rufe filin jirgin saman Benghazi na tsawon ranaku, wanda hakan ya tilasta wa kasashe kwasar mutanensu ta jirgin ruwa. Kimanin Turkawa 25,000 ne ke zaune a Libiya, wadda ta kasance cikin Daular Usumaniyya.

Kafafen yada labaran gwamnatin China ma sun ce gwamnati na shirin kwasar Chinawa wajen 33,000 ta jiragen sama da na kasa da ma ta motoci daga Libiyar. Za a yi amfani da jiragen haya, da jiragen ruwan kamfanonin China, da jirahgen ruwan su a teku, da kuma motocin bus-bus. Kafafen yada labaran Girka sun ce gwamnatin Girka za ta taimaka wa China wajen kwasar Chinawa wajen 13,000 zuwa tsibirin Crete na yakin Mediterranean.

XS
SM
MD
LG