Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Gangamin Kin Jinin Gwamnati A Libya Sun Kafa Majalisar Kasa

Masu zanga zanga suke lalata hoton shugaba Gadhafi a Zawiya,ranar lahadi.
Masu zanga zanga suke lalata hoton shugaba Gadhafi a Zawiya,ranar lahadi.

Shugabannin gangamin kin jinin gwamnati a kasar Libya sun ce sun kafa Majalisar Kasa a biranen gabashin kasar da suka kwace daga hannun gwamnatin Muammar Gaddafi, a bayan fadan kwana da kwanaki da suka gwabza da dakaru masu yin biyayya ga shugaban na Libya.

Kakakin majalisar, Hafiz Ghoga, ya fada jiya lahadi cewa wannan majalisa zata zamo kamar fuskar juyin juya hali ce, amma ba wai zata taka rawar gwamnatin rikon kwarya ce ba.

A can yankin yammacin Libya kuma, masu zanga-zangar kin jinin gwamnati sun kama garin Zawiya mai nisan kilomita 50 daga Tripoli, babban birnin kasar. An ce masu zanga-zangar su na daura damarar fatattakar farmakin da ake sa ran dakaru masu biyayya ga shugaba Gaddafi zasu kai a bayan da suka kewaye garin.

‘Yan jaridu na kasashen yammaci da suka kai Zawiya sun ce daruruwan mutane sun hallara a tsakiyar garin jiya lahadi su na rera baitocin kin jinin shugaba Gaddafi. ‘Yan jaridar sun bada rahoton barna mai yawa da suka gani daga fadan da aka gwabza kwanakin baya, inda suka ga alamun harsasai a jikin gine-ginen da wasu sun kone, da kuma garewanin motocin da aka kona a kan tituna.

A jiya lahadin, shugaba Gaddafi yayi watsi da masu adawa da shi, yana mai fadin cewa mutane ne ‘yan kalilan wadanda sojojinsa sun riga sun kewaye su.

A bayanin da ya bayar ta wayar tarho ga gidan telebijin na Pink na kasar Serbia, ya kuma yi tur da takunkumin da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kafa ranar asabar a kan Libya saboda matakan ad gwamnatinsa ta dauka na kai farmaki a kan ‘yan zanga-zanga.

XS
SM
MD
LG